September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

ISWAP ta nemi Najeriya ta biya fansar sama da N190m kan ma’aikatan agaji

2 min read

Cikin wani hoton bidiyo da ƙungiyar ta fitar a farkon makon nan, an nuna waɗanda aka kama na rokon gwamnatin Najeriya ta kuɓutar da su.

Mutanen sun hadar da wani jami’in ƙungiyar agaji ta Action Against Hunger da na ƙungiyar Reach International da kuma na International Rescue Commitee da wani jami’in hukumar ba da agaji ta SEMA hadi da wani jami’in tsaro mai zaman kansa.

Wata sanarwa da kungiyar agaji ta Action Against Hunger ta fitar na cewa an kama mutanen ne tun a watan jiya,.

Ko da a shekarar 2019, sai da ƙungiyar ISWAP ta kashe wasu ma’aikatan jin ƙai guda shida na ƙungiyar Action Against Hunger da ta yi garkuwa da su.Wani mai bincike kan ayyukan ƙungiyoyin ta-da-ƙayar-baya a Afirka, Barista Bulama Bukarti, ya faɗa wa BBC cewa ya danganta da wanda aka kama, akwai wadanda ake biya akwai kuma waɗanda ba a biya.Ya bayyana cewa lamarin abin takaici ne, domin biyan kudin zai iya bai wa mayakan ƙarin ƙwarin gwiwa don sake kama wasu mutanen da za su ci gaba da neman kuɗin fansa a nan gaba.

Sai dai ya ce ƙin biyan kuɗn kuma zai iya janyo halaka ma’aikatan agajin kamar yadda hakan ta sha faruwa a baya.

To sai dai ɗaya daga cikin kungiyoyin da aka kama jami’an su wato Action Against Hunger, ta ce tana ƙoƙarin ganin ta ceto nata jami’in.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *