July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar Daliban karamar hukumar Dala wato Dala local Government Students Association tayi kira da kyakkyawar murya

2 min read

Kungiyar Daliban karamar Hukumar Dala wato Dala Local Government Students Association,ta bukaci kungiyoyin dalibai dasu zama masu nuna da’a da bi yayya a duk inda suka tsinci kansu.
Sabon Shugaban kungiyar Kwamared,Ibrahim Mijinyawa ne ya bayyana haka jinkadan bayan kamala karbar rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kungiyar,wanda ya gudana a sakatariyyar kungiyar da karamar hukumar Dala a nan Kano.
Shugaban ya kuma ce dalibai na da muhimmanci ga rayuwar al’umma inda ya ce ilimi shi ne kashin bayan ko wacce irin al’umma a dan haka akwai bukatar matasa maza da mata su kara dage dantse.
Kwamared Ibrahim Mijinyawa ya kuma bayyana cewa kungiyar zata hada kai da sauran mambobinta domin ciyar dalibai ‘yan asalin karamar hukumar gaba.
A nasa jawabin Sanatan Kungiyar Kwamared Abba Mansur Saraki ya ce daga cikin abubuwan da suka sanya a gaba hadda bawa masu bukata ta musamman fifiko a cikin lamuran kungiyar.
Sanata Abba Mansur Saraki yay a sha alwashin bawa dukkan daliban Dala gudunmawar data da ce domin samin ci gaba mai daurewa a tsakaninsu.
Wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya ruwaito cewa cikin wadanda aka zaba a yau sun hadar da Ibrahim Mijinyawa a matsayin shugaban kungiyar da kuma Sakataren kungiyar Kwamared Shareef Yusuf Sani
da sauran shugabanni da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *