June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Labarin Wasannin tsakiyar Mako.

2 min read

Manchester United ba za ta biya sama da £50m don sayo dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho ba. Sai dai Dortmund tana so ta sayar da dan wasan mai shekara 20 kan fiye da £100m. (Sky Sports)

Arsenal na duba yiwuwar yin amfani da dan wasan Faransa Matteo Guendouzi, mai shekara 21, a wani bangare na musayar ‘yan kwallon kafa a lokacin musayar da za a yi a bazara. (Mail)

Tottenham tana da kwarin gwiwar dauko dan wasan Southampton da Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 24, a bazara amma sai ta soma sayar da wasu ‘yan wasan tukuna. (Telegraph – subscription required)

Manchester City tana shauƙin dauko dan wasan Bournemouth da Netherlands Nathan Ake. Amma za ta iya fuskantar kalubale daga Chelsea, wacce ita ma take son dauko dan wasan mai shekara 25. (Athletic – subscription required)

Dan wasanBarcelona Marc Jurado, dan shekara 16, ya bar kungiyar. Ana sa ran dan wasan na Spaniya zai komaManchester United a bazara. (ESPN)

Benfica na son Pochettino, Ina Aguero zai koma?
Valencia ta kori kocinta Albert Celades
Juventus ta kara kaimi a yunkurin da take yi na dauko dan wasan Valencia Ferran Torres, dan shekara 20. Ana rade radin cewa dan wasan na Spaniya zai koma Manchester United ko Borussia Dortmund. (Mail via Onda Cero)

An hango dan wasan Real Madrid daMorocco Achraf Hakimi, mai shekara 21, a Italiya gabanin shirin komawarsa Inter Milan a kan £36m. (Mail)

Roma ta tabbatar da rahotannin cewa ta tsawaita zaman aronHenrikh Mkhitaryan wanda ta karbo daga Arsenal zuwa karshen kakar wasan bana. Dan wasan na Armenia mai shekara 31 ya koma Roma ne a watan Satumbar da ya wuce. (Evening Standard)

Manchester City ta kammala yarjejeniyar da take kullawa inda za ta karbo dan wasan Spaniya mai shekara 18 Pablo Moreno daga Juventus, yayin da za ta bayar da dan wasan Portugal Felix Correia, mai shekara 19. (Guardian)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *