June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutane 17 ne suka mutu a jiya Talata a Nigeria.

2 min read

An ƙara gano masu cutar korona 561 ranar Talata a Najeriya, lamarin da ya sa yawan masu cutar a ɗaukacin ƙasar ya kai 25,694.

Duk da sassauta matakan kulle da hukumomin ƙasar ke ci gaba da yi, a baya-bayan nan dai NCDC kullum tana fitar da ɗaruruwan alƙaluman mutanen da suka kamu da cutar.

Sabbin alƙaluman da hukumar NCDC ta fitar a daren Talata, sun nuna cewa masu korona goma sha bakwai ne Allah Ya yi wa rasuwa cikin sa’a 24 a Najeriya.

Mafi yawan mutanen da aka sake ganowa cutar ta shafa sun fito ne daga Lagos, jihar da annobar ta fi ƙamari a ƙasar, da mutum 200. Yanzu yawan masu cutar korona a Lagos, ya haura 10,500.

Duk da haka, masu korona 344 ne suka warke a jiya Talata, har ma kuma an sallame su daga cibiyoyin killace masu jinya na ƙasar.Jihar Edo, ta sake gano sabbin masu korona 119 ranar Talata. Sai Kaduna, inda mutum 52 suka sake kamuwa. Daidai da adadin na Abuja.

A Neja, an korona ta sake harbin mutum 32, sai jihar Ogun mutum 19. Ondo, 16. Da kuma 14 daga jihar Imo.

Haka zalika, an ba da rahoton sake samun mutum 11 da cutar a jihar Filato ranar Talata. Sai jihohin Abia da Oyo, inda aka gano mutum takwas-takwas cikin kowaccensu.

Akwai mutum bakwai a jihar Bayelsa, sai Katsina mai mutum shida. Kano na da sabbin masu cutar biyar.

Jihohin Bauchi da Osun da Kebbi, dukkansu an sake gano mutum uku-uku ɗauke da korona a ranar Talata. Borno na da mutum biyu. Yayin da Jigawa ke da mutum ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *