June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Akwai yuhuwar Majalisun tarayyar Nigeria zasu dakatar da shirin samar da ayyukan yi ciki hadda Npower.

2 min read

Matakin ya zo ne kwana guda bayan ƙaramin ministan kwadago Festus Keyamo ya yi zazzafar jayayya da ‘yan majalisar lokacin da suka nemi ya yi musu bayani yayin wani zama da suka yi ranar Talata.

Haɗin gwiwar majalisar ƙwadagon ya buƙaci sanin hanyar da aka bi aka zaɓo ayarin mutum 20 daga kowacce jiha a Najeriya don yin aikin tantance mutanen da za a ɗauka aikin na wucin gadi.

Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, zaurukan majalisar sun bukaci kwamitocinsu na kwadago su gayyato babban ministan ayyuka na ƙasar Chris Ngige ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugaban kwamitin kwadago na majalisar wakilai Hon. Muhammad Ali Wudil ya shaida wa BBC cewa damuwarsu ita ce gwamnati ta bijiro da shirin ne don amfanin jama’ar da suke wakilta, don haka suke bibiya don ganin an yi adalci da tabbatar da daidaito.

Shirin N-Power: Ka-ce-na-ce ya kaure kan zargin babakere a kansa
Tambayoyin da aka fi yi game da aikin N-Power
“Dole mu bibiya mu tabbatar da yadda aka yi aka zaɓo ayarin mutum 20 da za su yi aikin ɗauko matasan da za su ci gajiyar shirin,” in ji ɗan majalisar.

Ya ce sun nemi a dakatar da shirin ne saboda a matsayinsu na majalisa suna da haƙƙi a yi musu bayani don su tabbatar an yi daidaito.

Ministan ya zargi ‘yan majalisar da ƙoƙarin karkatar da shirin da ofishinsa ya ɓullo da shi don cin moriyar masu ƙaramin ƙarfi.

Wasu rahotanni ma sun ambato Festus Keyamo na cewa jayayyar ta taso ne saboda ‘yan majalisar sun buƙaci sai ya ba su ƙari a kan kashi 15% da ya ware musu tun da farko, abin da shi kuma ya ce ba za ta saɓu ba.

Shi dai Muhammad Ali Wudil ya ce ministan ya shaida musu a yayin zaman ranar Talata cewa ‘yan majalisar ba su da ikon su tambaye shi game da yadda aka zaɓo mutanen da za su ɗauki ma’aikatan.

Sun nemi kashi 15% a cikin duk mutum 1,000 da za a ba aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *