June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kara farashin kudin manfer a Nigeria.

2 min read

Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan tsananin rayuwa a sanadiyyar annobar cutar COVID-19, kwatsam karin kudin man fetur ya bayyana daga hukumar PPPRA.

A wata sanarwa da ta bayar ga masu hada-hadar sayar da mai a kasar, hukumar ta bada shawarar a sayar da man fetur a tsakanin Naira 140.80 ko Naira 143.80, bayan da ta yi nazari akan hidindimun da ke cikin kasuwar sayar da man.

Hukumar ta PPPRA ta ce ta yi la’akari ne da hidindimun da suka hada da kudin dako na jiragen ruwa da na mota da kuma alawus-alawus da wasu kananan kashe-kashen kudade da ake yi domin samar da man ga jama’ar kasa.

Mataimakin Shugaban Kungiyar masu sayar da man fetur ta Najeriya IPMAN, Abubakar Maigandi Dakingari, ya ce wanan mataki ya saba wa lokaci kuma bai yi masu dadi ba saboda sai sun sake neman wasu makudan kudade kafin su sayo man da za su sayar wa jama’a, ga shi yanzu babu kudi a hannun mutane a cewarsa.

Da ya ke nasa tsokacin, tsohon mukaddashin shugaban kungiyar ma’aikatan Mai ta Najeriya, Kwamared Isa Tijjani, ya ce dama abin duk yaudara ce. Ya kara da cewa ya kamata a yi maza-maza a gyara matatun man da kasar ke da su guda hudu saboda a daina yaudarar mutane akan farashin mai, domin ana ta yawo da hankalin jama’a a daidai lokacin da ake fama da annoba a duniya.

Abin jira a gani shi ne ko za a amince da shawarar a yi karin ko akasin haka a daidai lokacin da farashin man ke kwan-gaba-kwan-baya a kasuwar duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *