July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ana zargin dagacin Yalwa da cinyewa wasu manoma gonakansu.

2 min read

Al’ummar garin Yalwa da ke karamar hukumar Rano, sun bukaci masarautar Rano da ta karbar musu gonakinsu wanda suke zargin dagacin garin Yalwa ya kwace.
Mutanen sun ce, sun gaji gonakin ne daga iyaye da kakanni, amma kwasham sai suka tarar wasu mutane na noma a cikin
Kamar yadda mutanen suka bayyana, suna zargin dagacin garin Yalwa, Isah Usman Shehu da karbe musu gonaki wanda tuni ya bada umarni fara noma a ciki, sannan kuma yana musu barazana da rayuwarsu a duk lokacin da suka masa magana akan hakkokin na su.
Abdulmuminu Sulaiman wanda aka fi sani da Kankau, na daga cikin wadanda dagacin garin Yalwan yasa aka kulle har na tsawon watanni tara, ya karin haske kan al’amari, Alhaji Abubakar Sadiq Dan uwa ga kankau, shi ma ya bayyana abun ya sani gamida batun inda ce tsantsar zalinci ne kawai domin kuwa kusan mutane 10 sun kawo masa korafin sa.
Ya kuma sha alwashin biwa kafatanin mutanan hakkinsu domin barin irin mutanan suna shugabantar mutane babban hatsari ga rayuwar al’ummar domin shugabanci abune da Allah ya umarta kuma batare tauyewa al’umma hakkinta ba.
Jin wannan koken ne yasa muka so jin tabakin Dagacin garin Yalwa Isah Usaman Shehu wanda bai yadda a nadi muryarsa ba, cewa ya yi ba zai ce komai ba, har sai ya samu umarnin daga Hakimi, ko da muka tuntubi Hakimin Mannir Abubakar Tafida ila, ya shaida mana cewa, a yanzu haka bincike suke akan al’amarin don daukan mataki na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *