July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnan Jihar Kano a tarayyar Nigeria ya jagoranci Kwamitin yakin neman zaben Edo.

1 min read

Jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben jihar Edo.

Kwamitin — mai kunshe da mambobin 49 — zai yi aike wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a cewar sanarwar da jam’iyyar ta fitar dauke da sa hannun mataimakin sakataren yada labarai na kasa Yekini Nabena.

Gwamnan Jihar Imo Senata Hope Uzodima ne zai kasance mataimakin Ganduje, sai kuma Honourable Abbas Braimoh a matsayin sakataren kwamintin yakin neman zaben.

Ab kafa kwimitin ne bayan amincewar shugabanta na riko gwamanan Yobe Mai Mala Buni a zaben da ake sa ran gudanarwa a ranar 19 ga watan Satumba 2020.

A ranar Litinin 6 ga watan Yuli, jam’iyyar za ta kaddamar da soma aikin kwamitin a Abuja.

Article share tools

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *