Gwamnatin Kano ta ce za’a koma makarantu tare da hana tallah a fadin jihar baki daya.
1 min read
Gwamnan Kano Abudllahi Umar Ganduje ya janye dokar kulle da ke aiki a jihar.
Ma’aikatar lafiya ta jihar ce ta sanar da hakan a shafinta na tuwita ranar Alhamis.
Gwamnatin ta ce ma’aikata daga mataki na 12 zuwa sama za su koma aiki daga ranar Litinin 6 ga watan Yuli.
Sannan ana ci gaba da tattauna wa kan ranar da za a bude makarantu ga dalibai da ke shekarar karshe da masu rubuta jarrabawar kammala aji uku da ‘yan firamare masu rubuta jarabawar shiga sakandare.
Haka zalika cire wannan doka na nuni da cewar an bude dukkan guraren da aka kulle a baya amma dole su tabbatar da matakan kariya a guraren harkokinsu kamar yadda hukumomin lafiya suka umarta, a cewar kwamishinan yada labarai na Kano Malam Muhammad Garba