June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan Jarida Na Bukatar Karin Albashi a Najeriya – Mohammad Garba

2 min read

Rashin albashi mai kyau, da rashin cikakkiyar kula da walwala, da kare hakkokin ‘yan jarida a Najeriya na daga cikin kalubalen da ma’aikatan aikin jarida da yada labarai ke fuskanta a kasar.

Duk da cewa masu ruwa da tsaki a bangaren kamar majalisar kula da ayyukan ‘yan jarida ta kasa, da kungiyar editoci, da kuma kungiyar ‘yan jarida ta NUJ, har ma da masu sharhi da rajin ci gaban aikin jarida a Najeriya sun dade suna gwagwarmayar wayar da kan hukumomi game da muhimmancin samar da tsarin da ya dace ga ‘yan jarida, amma har yanzu a iya cewa kwalliyya ba ta kai ga biyan kudin sabulu ba.

Tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya kuma kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Mohammed Garba, ya ce ya kamata kungiyoyin ‘yan jarida a Najeriya su tashi tsaye wajan ganin an kara musu albashi, duba da yadda wasu kafofin yada labarai masu zaman kansu ba sa biyan albashi mai tsoka ga ma’aikatansu.

Kwamared Mohammed ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano na kokarin samar da tsarin albashi na musamman ga ‘yan jarida a jihar.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da masana a fannin yada labarai da aikin jarida ke sharhi akan kalubalen da annobar COVID-19 ta haifar ga kafofin yada labarai a Najeriya da sauran sassan duniya.

Janar Manaja na Radio Vision FM a Kano, Malam Adamu Ladan, ya ce annobar cutar COVID-19 ta kawo kalubale sosai ga kafofin yada labarai duba da yadda wasu kamfanoni suka rufe kuma ba a samun kudaden shiga sosai daga tallace-tallace, lamarin da ya sa kan dole wasu kafofin labaran suka rage ma’aikatansu da wasu ayyuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *