June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Dalilin Dakatar Da Shirin Daukar Matasa Aiki a Najeriya

2 min read

A karon farko cikin shekara daya da Majalisar Dokokin Najeriya ta kama aiki, an samu takaddama da ta kunno kai har ya sa Majalisar ta ce ta dakatar da shirin da Gwamnati Tarayya ta yi na daukan matasa 774,000 aiki a jihohi 36 na kasar.

Wannan ya biyo bayan wata mahawara mai zafi da ta faru tsakanin Ministan Kwadago na Kasar Fetus Keyamo da Kwamitocin Majalisar.

Bayan hurumin da majalisar dokokin kasa ta dauka a kokarin da Gwamnati ke yi na daukan ma’aikata daga kowacce karamar hukumar da ke kasar, wanda majalisar ta ce, dole sai da sa hannunta cikin al’amarin.

Majalisar ta gurfanar da karamin Ministan Kwadago Festus Keyamo don sannin hanyar da za a bi wajen tabbatarwa da jama’ar da suke wakilta sun amfana da wannan dama.

Amma Minista Keyamo ya yi biris wajen ba da bayani inda ya ce, majalisar tana nema ta wuce gona da iri.

Keyamo ya kara da cewa, sun nemi a yi zaman cikin sirri ne, amma shi kuma ya ce, dole a yi a bainar jama’a kuma a gaban ‘yan Jaridu.

Amma mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Ajibola Basiru ya ce, Majalisa ba ta gamsu da bayanan Ministan ba, saboda haka sun dakatar da shirin daukar aikin sai sun samu bayanai da ya gamsar da su tukunna,

Amma idan shugaba Buhari bai amince da matakin nasu ba, yana iya kalubalantar su a Kotu.

Kwararre a fannin kundin tsarin mulkin kasa, Barrista Mainasara Ibrahim ya ce, Majalisa ba ta da hurumin dakatar da shirin duk da cewa su ne masu yin dokoki, sannan kuma su ne masu sa ido a bangaren gudanar da ayyuka.

Mai nazari akan al’aumuran yau da kullum, Alhassan Dantata Mahmood ya ce, baiwa ‘yan Majalisar guraben aiki abu ne da ake yi a matsayin na alfarma, amma babu dokar da ta ba da damar a ba su.

Wannan dai shine karo na farko da yake nuna fito na fito tsakanin majalisar ta 9 da bangaren shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *