July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Labarin wasanni daga Bustandaily.

2 min read

ENGLAND – PREMIER LEAGUEJULY 2
FT
Sheffield United
3 – 1
Tottenham Hotspur
FT
Manchester City
4 – 0
LiverpooSPAIN – LALIGA SANTANDERJULY 2
FT
Eibar
0 – 2
Osasuna
FT
Real Sociedad
2 – 1
RCD Espanyol
FT
Real Madrid
1 – 0
Getafe
ITALY – SERIE AJULY 2
FT
Atalanta
2 – 0
Napoli
FT
Roma
0 – 2
Udinese

Chelsea da Manchester City za su iya mayar da hankali kan dan wasan Everton dan kasar Faransa Lucas Digne, mai shekara 26, idan suka gaza dauko dan wasan Ingila Ben Chilwell, 23, daga Leicester. (ESPN)vEverton, Liverpool, Manchester City da Manchester United za su kallikwallon da Leon Bailey, mai shekara 22, zai murza ranar Asabar yayin da dan wasan na Bayer Leverkusen da Jamaica yake sha’awar komawa Ingila. (Sky Sports)

KocinManchester City Pep Guardiola yana son dauko dan wasan Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29; da dan wasan Villarreal dan kasar Sufaniya Pau Torres, mai shekara 23; da kuma dan wasan Benfica da Portugal Ruben Dias, mai shekara 23, a yayin da yake son karfafa bayan kungiyar. (Times – subscription required)

Sevilla tana son karbo aron golan Chelsea da Sufaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25, wanda makomarsa ba ta da tabbas a Stamford Bridge. (Sun)

Manchester United ta amince dan wasan Ivory Coast Eric Bailly, mai shekara 26, ya tafi zaman aro a kakar wasa mai zuwa, a daidai lokacin da Valencia take son dauko dan wasan na baya. (Sun)

Arsenal na zawarcin Griezmann
Inter ta dauko Hakimi daga Real Madrid
GolanManchester United wanda yake zaman aro a Sheffield United, Dean Henderson, mai shekara 21, ya yi gargadin cewa ba zai ci gaba da zama a kungiyar ba idan ba ta mayar da shi matsayin gola na farko a wasanninta ba, a yayin da Chelseatake son dauko dan wasan.(Express)

Chelsea tana son dauko golan Lille mai shekara 24 Mike Maignan da Alphonse Areola, mai shekara 27, wanda yake zaman aro aReal Madrid dagaParis St-Germain. (Express)

Sai dai ita ma Tottenham tana duba yiwuwar zawarcin Maignan a bazara, inda Jose Mourinho yake so ya maye gurbin golan Faransa Hugo Lloris, mai shekara 33, da shi. (Sun)

Tsohon kocin Aston Villa Tim Sherwood ya yi amannar cewa kyaftin din Villa Jack Grealish, mai shekara 24, zai komaManchester United a bazarar nan. (Birmingham Mail)

Dan wasan Ingila Angel Gomes, dan shekara 19, yana duba yiwuwar tafiya kasashen wajen ko da yake bai kulla wata yarjejeniya a can ba bayan Manchester United ta sake shi. (Manchester Evening News)

Kocin Tottenham Jose Mourinho ya ce ba zai yi musayar dan wasan Argentina Giovani Lo Celso, mai shekara 24, da dan wasan Manchester United Bruno Fernandes ba, bayan Tottenham ta gaza dauko dan wasan Portugal a bazarar da ta wuce. (Sky Sports)

Sheffield United tana son dauko dan wasan Ghana Abdul Mumin, mai shekara 22 daga FC Nordsjaelland a bazarar nan. (Mail)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *