July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Matasa na samun matsala akan rijistar Npower.

2 min read

Matasa da dama a nan Kano na kokawa da irin yadda matakan han cunkoso a cikin gine-ginen bankunan kasuwanci ke dauka kafin saurarar abokan huldarsu ke haddasa dogwayen layuka a dukkan ressan su da ke nan Kano.
Wasu matasa da lamarin ya rutsa da su, sun kuma yi zargin cewa matakin ya haddasa dandazon mutane a bankin tsawon kwanaki biyu suna zuwa daya daga cikin bankunan don karbar lambar nan ta sirri, wato BVN da nufin samun damar shiga shirin gwamnatin tarayya na N-Power wanda dole sai da lambar ne za a samu shiga amma har yanzu bas u samu ba
Matasan maza da mata sun shaidawa Bustandaily cewa rashin mallakar BVN din na barazanar hana su damar cin moriyar shirin na N-Power kasancewar tana cikin sharuddan da ake bukata kafin daukar mutum.
Su zargin bankunan da yin amfani da umarnin gwamnati ta shinfida na tabbatar da tazara tsakanin mutane tare da sanya takunkumin hanci da baki.
Haka kuma suka ce matsalar ta kara tsanani ne musamman saboda rashin ingantaccen layin intanet mai karfi.
Jaridar Bustandaily ta jiwo daga wasu daga cikin jami’an wasu daga bankunan sai dai sun ce ka’idar aikinsu bata ba su damar yin magana da ‘yan jarida ba.
Wata majiya ta ce matasan da basu da lambar sirri nan ta BVN suna da yawan da sai an yi shiri na musamman don samar musu da lambar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *