September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sai an koma ga Allah sannan corona zata yi sauki

1 min read

Limamin Masallacin Juma’a na Abdullahi Bn Abbas da ke unguwar Sani-Mainagge a nan birnin Kano, Malam Isma’il Abdulsalam Muhammad ya hori jama’a da su rinka gudanar da salloli kamar yadda musulunci ya koyar.
Malam Isma’il Abdulsalam Muhammad ya yi wannan horo ne yau bayan kamala sallar Juma’a da ya gabatar a masallacin.
Limamin ya ce akwai fa’idoji masu yawa da Karin nasarori da ubangiji ya tanadarwa masu tsayar da salla kamar yadda manzon tsira SAW ya koyar.
Ya kara da cewa ubangiji na saukar da annoba kan bayinSa, don hakan ya sanya musulmi komawa gareshi, kasancewar zunubai sun da yawa musamman a wannan lokaci da mutane ke aikatawa.
limamin na kira ga musulmi da su rinka yawaita sadaka da taimakon jama’a don kuwa hakan na sanadin samun waraka daga kowace irin annoba da ma sauran wasu matsalolin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *