Shugaban kasa ya amince da gabatar da wasu ayyukan raya kasa
2 min read
Shugaban kasa Buhari ya amince da wasu ayyuka da suka tasamma Naira bilyan 20.36 yayin taron majalisar zartaswa ta kasa FEC da ake yi kowane mako. Gwamnatin tarayyar ta amince da ware kudi N20, 366, 454, 990 domin yin wasu ayyuka na gyara hanyoyi da wani titin jirgin sama a zaman na jiya.
Gwamnatin tarayya za ta kashe wannan kudi ne a ma’aikatu hudu kamar yadda mu ka samu labari daga gidajen jaridun Najeriya a ranar Laraba, 1 ga watan Yulin 2020.
Bayan an kammala ganawar shugaban kasa Muhammadu Buhari da jami’an gwamnatinsa, wasu Ministoci sun bayyyana cewa takardun da su ka gabatar a majalisar FEC sun samu shiga.
Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola, ministan babban birnin tarayya Abuja Muhammed Bello, ministan harkar ruwa Suleiman Adamu da ministan harkokin jiragen sama Hadi Sirika, su ka bayyana wannan.
Muhammed Bello ya ce an yi na’am da wasu takardu biyu da ya gabatar gaban shugaban kasa na yin titi daga Yaba zuwa Gurdi a cikin yankin Abaji da kuma aikin hanyoyi a cikin garin Abaji.
Sanata Hadi Sirika ya ce Gwamnatin tarayya ta amince da aikin hanyar motocin haya a cikin babban filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagos.
Aikin dai zai ci Naira biliyan 2.3, ma’aikatar ruwa ta gabatar da takardun neman kwangilar gyara cibiyar noman rani da ke garin Lankang a jihar Plateau. FEC ta kuma amince da wannan kwangila a kan Naira miliyan 634.2.