July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yan kasuwa za suyi asarar sama da dala bilyan biyu – ITC

1 min read

‘Cibiyar kasuwanci ta Duniya (ITC), ta yi hasashen cewa, masu fitar da kayayaki ketare ‘yan nahiyar Afirka, ka iya asarar dala bilyan biyu da miliyan dari hudu sakamakon ci gaba da yaduwar annobar cutar COVID-19.

A cewar cibiyar rufe masana’antu a kasar China da nahiyar Turai da kuma Amurka, sun sanya masu fitar da kayayyaki ketare daga Afirka tabka asara mai dimbin yawa.

Cibiyar kasuwancin ta Duniyar ta ce kaso saba’in na wannan asarar ya faru ne sanadiyar rufe hanyoyin Turai, wanda masu fitar da kayayyakin ke bi.

Haka zalika cibiyar ta kuma ce masu fitar da kayayyaki ketare a Duniya baki daya, sun tabka asarar dala biliyan dari da ashirin da shida.

Mai rikon mukamin shugabar cibiyar kasuwancin ta Duniya Dorothy Tembo, ta ce wannan matsala ta faru ne sakamakon cutar COVID-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *