June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A cikin mako ɗaya mutum miliyan 3 sun nemi aikin N-Power – Sadiya Farouq

1 min read

Mutum miliyan uku ne suka cike neman gurbin aikin matasa dubu dari hudu na N-Power a cikin mako daya da aka bude yin rijistar shirin.

Ma’aikatar Agaji da Kyautata Rayuwar Al’umma ta ce zuwa ranar Juma’a 3 ga watan Yuli, mutum miliyan uku sun yi rijistar neman aikin N-Power, daga ranar Juma’ar 26 ga watan Yuni da aka kaddamar da shirin a karo na uku.

“Nan gaba kadan za a rufe shafin neman gurbin aikin domin a tantance matasan da za su amfana”, inji Mai Taimaka wa Darektan Yada Labarai na Ma’aikatar, Rhoda Iliya.

Karo na uku ke nan da mutanen ke neman aikin na N-Power suke yin rijista ta intanet yayin da matasan rukunin farko da na biyu ke bankwana da shirin.

A baya ministar ma’aikatar, Sadiya Umar Faruk ta sanar cewa ana shirin kawo karshen aikin wadanda suka amfana da shirin a rukunin farko da na biyu, inda ta nemi masana’antu masu zaman kansu su samar mu su aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *