July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kama mutumin da ya ci mutuncin mata a Saudiyya

1 min read

Jami’an ‘yan sanda a Saudiyya sun kama wani mutum da ya zagi matan kasar, yana cewa suna yin abubuwan da suka saba ladubban kasar, na basu damar yin sana’a da kuma zuwa aiki wurare daban-daban.

Kamar yadda jaridar Saudi Gazzete ta ruwaito cewa, mutumin na kalubantar aikin mata, kuma sukar da ya yi kan goyan bayan mata wajen sana’a a cikin al’umma, ya yi ta ne ta hanyar da hukumomi ba su ji dadi ba a tuwita, wanda kuma labarin ya yadu a kafafen sada zumunta.

Ta hanyar bibiyar shafin da aka wallafa labarin, jami’an tsaro sun gano bayanansa.

Mutumin dan asalin Saudiyya ne kuma shekarunsa sun kai 60 a yanzu haka yana karkashin kulawar jami’an tsaron kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *