September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kashe mutum 30 yayin satar shanu

1 min read

Hukumomi a Sudan ta Kudu sun tabbatar da kashe mutum 30 yayin wani hari da aka kai a jihar Jonglei da ke ƙasar a yunƙurin satar Shanu. Shugaban gudanarwa na yankin Elijah Manyok ya shaida cewa an shafe sama da sa’o’i biyar ana ɗauki ba daɗi a harin da aka kai a ranar Juma’a a “Duk Padiet Payam”. Ya bayyana cewa sama da mutum 40 ne suka samu raunuka kuma an sace shanu dubbai. A wannan shekarar dai an samu hare-haren ramuwar gayya da aka kai tsakanin al’ummomin Murle da kuma Lou Nuer. Tsakanin watan Fabrairu zuwa Mayu na wannan shekara, an bayar da rahoton cewa an kashe sama da mutum 800 sakamakon rikici a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *