June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ana zargin Sheikh Pantami ya saya wa matansa uku gidaje a Abuja.

1 min read

Ma’aikatar sadarwa ta Najeriya ta musanta wasu labarai da ke ta yawo a kafafen sada zumunta na kasar cewa Minista Dakta Ali Isa Pantami ya sayawa matanshi uku gidaje a Abuja.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar Uwa Suleiman ta fitar ta ce wannan batu ba shi da tushe balle makama.

Sanarwar ta ce “labarin jaridar intanet ta Sahara Reporters ta wallafa da ke zargin cewa ministan ya sayawa matansa uku gidajen a Abuja karya ne.

Tun da ministan ya kama aiki a bai sayi gida ko daya ba, kuma gidan da yake zaune ciki ya kama shi ne tun a watan Janairun 2017, shekara biyu kenan gabanin ya kama aiki”.

sanarwar ta kuma ce sauran gidaje biyun da jaridar ta wallafa ba ma a san daga inda ta samo su ba.

Bugu da kari ta yi kira ga al’ummar kasar da su yi watsi da wannan kokarin bata wa Minista Ali Pantami suna da ake kokarin yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *