April 15, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ma’aikatan kamfanin Bajaj 250 sun kamu da korona

1 min read

Ma’aikata a kamfanin Bajaj Auto, wanda shi ne kamfanin da ke kan gaba wurin ƙera babura da Keke Napep a Indiya, sun buƙaci shugabannin kamfanin da su rufe shi na ɗan wani lokaci, sakamakon mutum 250 da suka kamu da cutar korona.

Cikin waɗanda suka kamu, tuni biyu suka mutu. Shugabannin ƙungiyoyi a jihar Maharashtra sun ce mutane na tsoron zuwa wurin aiki. Kamfanin na da ma’aikata kusan dubu takwas.

Kamfanin ya ce za a ci gaba da aiki tare da ɗaukar matakai na kariya.

An kulle kamfanoni da dama bayan saka dokar kulle a fadin Indiya a ƙarshen watan Maris, kamfanonin sun shafe sama da watanni biyu a rufe.

Sama da mutum 600,000 suka kamu da cutar korona a Indiya, kusan mutum dubu tara cutar ta kashe a halin yanzu a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *