September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Man United ta koma ta hudu bayan doke Bournemouth 5-2

1 min read

Matashi Masson Greenwood ne ya ci wa United kwallo biyu masu kyau a gasar Premier da ta doke Bournemouth 5-2 a gasar Premier League ta koma ta hudu.Greenwood ne ya farke kwallon da Junior Stanislas ya fara cin Manchester United, bayana da aka koma zagaye na biyu ya ci kayataccen kwallo na gani na fada.

Hakan ya sa matashin dan wasan mai shekara 18 ya ci wa United kwallo 15 a kakar bana.

Marcus Rashford ne ya ci wa United na biyu a bugun fenariti, sannan Anthony Martial ya zura na uku a raga.

Manchester City za ta dauko Grealish
Sane ya rattaba kwantiragi da Bayern Munich
Bournemouth wacce take cikin ‘yan kasan teburi ta zare kwallo daya ta hannun Joshua King.

Haka kuma kungiyar da ta yi rashin nasara a wasa takwas a jere a waje ta zura wa United kwallo ta hannun Arnaut Danjuma, amma aka ce ya yi satar gida.

Bruno Fernandes ne ya ci wa United kwallo na biyar a bugun tazara, kuma United ta koma ta hudu a kan teburi kan Chelsea ta yi wasanta.

Chelsea za ta karbi bakuncin Watford a wasan na cin kofin Premier League da za su kara a Stamford Bridge.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *