July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wani fusataccen kare ya cinye wata jaririya ƴar kwanaki 26

2 min read

Wannan fusataccen kare ya kai wannan jaririya ƴar kwanaki 26 hari a lokacin da su ke kwance a ɗaki tare da ɗan uwan haihuwarta, a birnin Piripa da ke ƙasar Brazil, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta.

Jaririyar mai suna Anne ta kasance tagwaye ce, kuma tana kwance ne cikin dakin gidansu tare da ɗan uwan haihuwarta mai suna Analu, bayan da mahaifiyarsu ta zaga makota.

Tun da farko wasu rahotanni sun bayyana cewa mahaifiyar waɗannan tagwaye mai suna Elaine ta jiyo hayaniya a dakin da wadannan tagwaye ke kwance, wanda ta garzayo domin ta ga abin da ya ke faruwa, daga nan ne ta ga ashe karen su ne ya kai ƴaƴanta hari.

Elaine ta yi ƙoƙarin ɓamɓare Karen daga kan wannan jaririya, amma sai da taki ga kiran makociyar wacce ta ke malamar jinya ce, domin ta taimakata wajen korar karen.

Bayan sun samu nasarar korar karen ne su ka tarar ya yiwa wannan jaririya munanan raunika, inda a nan take aka fara bata agajin gaggawa, kafin daga bisani a garzaya da ita asibitin Maria Pedreira Barbosa domin ceton ran ta, a ƙarshe ta ce ga garinku nan.

Sai dai likitan da ya ke duba lafiyar Elaine lokacin da ta ke ɗauke da cikin ƴan biyun na ta, ya bayyana na ta a matsayin mace mai kula da lafiy arta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *