June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wani Gini yayi sanadiyar mutuwar wasu yara a unguwar Kuntau cikin karamar hukumar Gwale a nan Kano

2 min read

Ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ya sauka a Ranar Litinin din data gaba,a yayi nasadiyyar mutuwar Yara biyu,a yayin da hudu daga cikin su suka jikata a sakamakon fadowar wani gini a dai-dai lokacin da yaran suke neman mafaka domin kaucewa ruwan saman a Unguwar Kuntau din.
Shaidun gani da ido sun shaidawa Jaridar Bustandaily cewa ginin ya fadone a yayin da wata iska mai karfi ta taso a Ranar Litinin.
Daya daga cikin iyayen yaran da suka mutu, wanda kuma ya nemi da a sakaye sunansa ya ce” dan nasa suna tare dashi a gida kafin lokacin da Allah ya karfi ajalinsa, yace maganar karshe da sukai da marigayin ya ce dani yaushe zamu koma Makaranta a she maganar karshe muka yi dashi.
Haka zalika mahaifin yaran cikin kuka ya kuma ce ya dauki lamarin a matsayin kaddara ce babu wani mutum daya wuce kaddarar Allah.
Itama Hajiya Sadiya daya ce daga cikin mahaifiyar daya yaran da wannan gini ya fadowa wanda shima ya rigamu gidan gaskiya ta ce yaran nata ta aike shi ne shago ya siyo mata magi,shiru-shiru bai dawo ba,wanda ganin hadari ya taso yasa ta bazama neman sa,wanda a karshe a kayi sallama da ita cewa yaran nata ya rasu.
A yanzu haka dai ragowar yara hudu na kwance a asbiti, inda suke karbar magani kasancewar sun sami muggan raunika.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *