July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ƴan bindigar kan babura da suka addabi Arewacin Najeriya

2 min read

‘Yan bindiga masu amfani babura waɗanda ke zaune a dazukan da aka yi biris da su na ci gaba da kai hare-hare a wasu yankuna na arewa maso yammacin Najeriya.

‘Yan bindigar su ne na baya-bayan nan da suka shiga harkar garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa inda kuma suke matsa ƙaimi a hare-harensu.

Shekaru goma da suka wuce, an kashe sama da mutum 8,000 a jihohin Sokoto da Kebbi da Naija da Zamfara kamar yadda ƙungiyar nan da ke ƙoƙarin kare afkuwa da kuma sulhunta rikici ta International Crisis Group ta bayyana.

Sai dai hare-haren baya-bayan nan da aka kai a mahaifar shugaban Najeriya wato jihar Katsina inda aka kashe sama da mutum 100 tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni sun jawo zanga-zanga inda aka nemi shugaban ƙasar da ya yi murabus.vA hare-hare biyu daban-daban, ‘yan bindigar sun afka wa wasu ƙauyuka da suka samu tallafi daga gwamnati kan batun cutar korona yayin dokar kullen da aka saka.

“Su kusan 200 ne kan babura, kowane mai babur na ɗauke da fasinja kuma dukansu ɗauke da bindiga ƙirar AK 47,” in ji Bashir Ƙadisau, wani ganau wanda ya shaida wa BBC yadda lamarin ya faru.

Ya ce ya hau can saman bishiya bayan ya ga yawan baburan da suka tunkari garin na Ƙadisau, kuma ya ga masu harin na fasa shaguna da satar shanu da hatsi tare da harbe mutanen da suke guduwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *