Ana sanarda al’ummar musulmi rasuwar Hajiya Ladi Mudi yanzu a Makabartar Dan dolo.
1 min read
innalillahi wa inna ilaihi ra un Allah ya yiwa hajiya Ladi Mudi rasuwa mai kimanin shekaru 85 a duniya bayan ta sha fama da rashin lafiya.
Ta rasu ta bar jikoki da dama daga cikin jikokinta akwai Malam Usman Nagoda limamin masallacin Nana khadijah dake link 8 a unguwar bakin bulo.
Za’ayi Jana’izarta da misalin karfe 5:00 na yamma a makabartar dan dolo dake unguwar Gwauron Dutse.