Covid19: ‘Kulle ya durkusar da kananan masana’antu a arewacin Najeriya’
2 min read
Gwamnatin Najeriya ta yunkuro ta hanyar samar da wani tsari na tallafa wa masu kananan sana’oi da kasuwancinsu ya shiga wani hali sakamakon annobar korona.
Annobar korona dai ta girgiza bangarori da dama na rayuwar jama’a a fadin duniya musamman yadda tattalin arzikin kasashe ke ci gaba da fuskantar koma baya.
Sai dai kasashe da dama na kokarin tada komadar tattalin arzikinsu ta hanyar bijiro da tsare-tsare da za su habaka harkokin kasuwanci.
Dr Dikko Umaru Radda, shugaban hukumar bunkasa matsakaita da kananan masana’antu a Najeriya ya ce akwai tsarin tallafi da kuma rancen da Babban Bankin kasar ke bayarwa wadanda za su taimaka wa masu kananan sana’oi.v”Babban ciwon kanana da matsakaitan masana’antu na kasarnan in ka tambaye su shi ne, rashin samun kudaden da za su gudanar da ayyukansu. Kuma an fito da wani shiri wanda Babban Bankin kasar) ya fito da shi wanda ake ba da tallafin naira miliyan daya zuwa miliyan 10,”
“Abin da kake bukata ka je hukumar da ke horar da kananan da matsakaitan masana’antu a tabbatar da an horar da kai, wannan takarda ta horarwa ita ce babban ginshiki na wannan bashin da za a baka.”
A cewarsa, korona ta shafi tattalin arzikin duniya musamman a Najeriya da kusan mutum miliyan 60 na ‘yan kasar sun dogara ne kan kananan da matsakaitan sana’oi.
“A Najeriya, muna da kusan mutum miliyan 41,500,000 wadanda masu yin kananan da matsakaitan masana’antu ne, kuma abin da ya mayar da Najeriya ta samu matsala, shi ne kusan wannan adadi miliyan 40 da wani abu ‘yan kananan masana’antu ne wadanda jarinsu karami ne a kauyuka suke.”Ya kuma ce nnoba da ta zo ta taimaka wajen ganin cewa sun cinye jarinsu, wasu sana’arsu ta kare saboda (kulle), amma kusan tallafin da gwamnati ke fito da su za ka ga ana kallon kanana da matsakaitan masana’antu, wadanda za ka su ba sa ma da abin da za su iya zuwa banki su iya samun wadannan basussukan da gwamnati ta ke, ba a basu mahimmanci kamar yadda ya kamata.
A ganinsa, irin wadannan masu karamin karfi ba bashi ya kamata a basu ba, “tallafi ya kamata a basu daga naira dubu 10 zuwa dubu 50 har 100 dai-dai gwargwadon irin abin da kake, ba karamin taimakawa zai yi ba.”
Ya ce sun ba da shawarwari ga wani kwamiti da ke karkashin mataimakin shugaban kasa na ganin yadda a kowace karamar hukuma, “an dauki masu irin kananan sana’oi kusan dari 500 a kananan hukumomi 774 a basu tallafin ko da dubu 50 ne don ganin cewa sun bunkasa tattalin arzikinsu kuma mafi yawan wadannan mutane suna arewacin Najeriya.”