September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Daga yanzu ba lallai sai matan saudiyya sun saka Abaya ba – Sarki Salman

2 min read

Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gado ya ce daga yanzu sanya Abaya ba dole ba ne. Yariman Salman ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke tattaunawa da gidan Talabijin na CBS da ke kasar Amurka.
Ya ƙara da cewa mata ba sa bukatar sanya zumbuleliyar rigar, suna bukatar a dama da su a fagen suturar zamani matukar kayan ba sa nuna tsiraici don haka ba lallai sai sun sanya abaya ba.
Ya ce kawai abinda ake da bukata shi ne Mata su sanya sutura mai kyau da zata iya rufe musu tsiraici.
Tun da farko wasu daga cikin matan Saudiyya ne su ka yi bore don nuna adawa da tilasta musu sanya abaya, wadda dogowar riga ce da ke rufe tun daga sama har kasa da suke sanyawa a lokacin da za su fita bayyanar jama’a.
Hukumomin ƙasar Saudiyya na da tsaurin ra’ayi kan suturar da matan kasar ke sanyawa wadda za ta rufe baki dayan jikinsu a bainar jama’a, inda suke sanya abaya matukar musulmi ne.
Ana ganin cewa Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gado yana kawo sauye-sauye a faɗin kasar musamman a bangaren ƴancin mata da kuma nishadantarwa.
Domin ko a cikin watan Satumbar 2018 sai da gwamnatin Saudiyya ta sanar da dage haramcin tuki ga mata , kuma tuni aka fara bai wa matan lasisin tuki a Saudiyya.
Kafin dage haramcin Saudiyya ta kasance kasa ta karshe a duniya da mata ba su da izinin yin tuki.
Kasar Saudiyya dai kasa ce da ta ginu kan al’amuran addini, kuma wadannan sauye-sauyen suna alamta yadda kasar ke sauya wa cikin sauri zuwa ga rayuwar da ake yayi a kasashen Turai.
Sai dai wadannan sauye-sauyen da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman yake bullowa da su a kasar, na sanya mutane cikin rudani da jawo ce-ce-ku-ce ba a Saudiyyar ba har ma a sauran kasashen musulmai na duniya.
Ana kallon Saudiyya a matsayin wata jagora ta addinin musulunci, shi ya sa a duk lokacin da ta bullo da wani abu da ba a saba gani ba yake darsa shakku a zukatan wasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *