July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Dan Najeriya Ya Maida Kudin Tsintuwa, Ya Ki Karbar Tukwici

1 min read

Wani dan Najeriya da ke karatu a Japan ya tsinci wasu “makudan kudade” ya kuma mika su ga ‘yan sandan kasar.

Wata sanarwa da kakakin fadar gwamnatin Najeriya Femi Adesina ya fitar a yau Asabar, ta ce Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aiki da sakon gaisuwa da jinjina ga Ikenna Nweke, wanda har ila yau, ya ki karbar tukwici daga hannun hukumomin kasar bayan da aka yi masa tayi.

Sanarwar ba ta ambaci adadin kudaden da Nweke ya tsinta ba, amma ta ce “makudan kudade ne a cikin ‘yar jakar kudi da ake sakawa a aljihu.”

“Shugaba Buhari na yin jinjina ga Nweke, saboda hali na gaskiya, sanin ya kamata da wadatar zuci da ya nuna.” Sanarwar ta Adesina ta bayyana.

Kakakin fadar gwamnatin Najeriya ya kara da cewa, “halaye na gari dabi’a ce da aka san ‘dan Najeriya da su, ba aikata miyagun ayyuka ba.”

Nweke dalibi ne a Jami’ar Tsukuba da ke kasar ta Japan, wanda har ila yau ya ke karantarwa.

“Lallai ka nunawa duniya cewa ‘yan Najeriya suna da kyawawan halaye na koyi.” Wasikar da aka aikawa Nweke wacce daya daga cikin hadiman fadar shugaban Najeriya Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter a yau Asabar ta ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *