June 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ruwan sama na barazana ga rayuwar mu iji mai unguwar Tudun Yola.

1 min read

Mai Unguwar Tudun Yola a nan birnin Kano, Alhaji Kabiru Shehu Abdullahi, ya bukaci gwamnatin Kano da ta gina musu magudanan ruwa don karesu daga barazanar ambaliya ruwa a daminar bana.
Alhaji Kabiru Shehu Abdullahi ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya Lahadi
Wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya ziyar ci Unguwar ta Tudun Yola ga kuma rohoton da ya dama.
Mai unguwar ta Tundu Yola ya ce a duk shekara suna gudanar da aikin gayya a lokacin damina don gyara magudanan ruwan amma lamarin yafi karfinsu.
Alhaji Kabiru Shehu ya kara da cewa hatta manyan titin Unguwar babu wata hanya guda daya a yanzu wanda ruwan sama idan ya sauka zai sami hanyar wucewa kai tsaye, inda ya ce daga fara ruwan wannan damuna an samu rugujewar gidaje da shaguna da dama.
Wasu magidanta a unguwar sun bayyana cewa gidajensu na cikin matsala musamman yadda ruwan sama damunar bana yazo da wani irin yanayi wanda dole ne lamarin ya basu tsoro.
Haka zalika suma masu gudanar da kasuwanci a yankin sun bayyana kukansu,inda suka ce matukar basu sami daukin gaggawa ba ko shakka babu kasuwancin su zai iya fin karfinsu kasacewar shagunan suke inda suke dan samun na kaiwa bakin salati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *