Birtaniya za ta kakaba takunkumi kan mutane da kungiyoyin da suka taka rawa wajen cin zarafin bil’adama.
1 min read
Birtaniya za ta kakaba takunkumi kan mutane 49 da kungiyoyin da suka taka rawa wajen mummunan cin zarafin bil’adama shekarun da suka gabata.
Za a karbe kadarorin mutanen da ke Birtaniya, kan taka rawa a mutuwar lauyan nan dan Rasha Sergei Magnitsky a shekarar 2009e, a kuma haramta musu shiga kasar.
Haka kuma lamarin zai shafi ‘yan Saudiyya masu hannu a kisan dan jarida Jamal Khashoggi a shekarar 20018.
Wannan shi ne takunkumin da Birtaniya ta dauka na kashin kai ba tare da Tarayyar Turai ko Majalisar Dinkin Duniya ba.
Sakataren harkokin waje Domonic Raab ya ce matakin kakkausan sako ne aka aike.