Coronavirus a Najeriya: Mutum 544 sun sake kamuwa a Najeriya
1 min read
Alkalumman da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa cutar ta kara kashe mutum 11 cikin sa’a 24.
Yawan mutanen da a hukumance annobar korona ta shafa yanzu sun kai 28,711 a Najeriya, yayin da kuma adadin wadanda cutar ta kashe suka kai 645 tun ɓullarta a ƙasar.
Adadi mafi yawa na masu korona da aka sake samu, ya fito ne daga Lagos, jihar da cutar ta fi ƙamari a Najeriya, inda mutum 199 suka sake kamuwa. kuma Yanzu yawan masu korona a jihar ya kai 11,244.