‘Kamaru za ta fuskanci ruwan sama mai karfi da ambaliya’
1 min read
ukumar kula da yanayi a Kamaru ta yi hasashen cewa za a samu saukar ruwa mai yawa fiye da kima a mafi yawan sassan kasar.
A cewarta ruwan da ya riga ya fara sauka a watan Yuni ka iya kai wa har watan gobe na Agusta.
Hakan kuma na iya haddasa ambaliya da za ta iya lalata tsirrai da wasu kayan abinci a cikin rumbuna.