June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Kwale-kwale ya kife da mutum 26 a Kogin Benue’

1 min read

Rahotanni daga jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya na cewa kwale-kwale ya kife a ruwa dauke da da mutum sama 20 a kogin Benue.

Wani dan uwa ga wadanda hadarin ya rutsa da su, Phillip Amos ya shaida wa BBC yadda lamarin ya faru inda ya ce hadarin ya faru ne lokacin da jirgin da ke dauke da fasinjojin ya nutse.

A cewarsa, wani mutum ya rasa ‘ya’yansa guda biyar a hadarin jirgin.

Ya ce “abin ba sauki, bai zo da sauki ba gaskiya, yanzu duk muna cikin bakin ciki ne kawai.”

Wasu rahotannin kuma na cewa lamarin ya faru a kogin Benue da ke wani kauye a Makurdi, babban birnin jihar.

Kawo yanzu dai hukumomi a jihar ba su ce komai ba game da lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *