Labari da dumi duminsa
1 min read
Rahotanni na nuni da cewa yanzu haka wuta ta tashi a gidan wutar lantarki dake unguwar Dan Agundi a nan Kano.
Wutar ta fara ne tin da misalin karfe 11 na safiyyar Litinin din nan wanda zuwa yanzu babu musabbabin tashin wutar.
Wasu shaidin gani da ido sun shaidawa wakilin Bustandaily yadda lamarin ya faru,wanda zuwa yanzu jami’an kasha gobara na kokarin shawo karshen lamarin.
Muna tafe da cikken bayani a nan gaba.