July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mataimakin shugaban APC Inuwa Abdulƙadir ya rasu

1 min read

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya (Arewa maso Yammacin kasar), Alhaji Inuwa Abdulkadir, ya rasu.

Iyalan marigayin sun tabbatar wa BBC Hausa cewa fitaccen dan siyarar na jihar Sokoto a rasu ne ranar Litinin da safe.

Sai dai ba a san sanadin rasuwarsa ba kawo yanzu.

Inuwa Abdulkadir, wanda ya taba rike mukamin Ministan Matasa na Najeriya, ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar APC .

Sai dai jam’iyyar, lokacin shugabancin Mr Adams Oshiomhole, ta taba dakatar da shi da Lawal Shu’aibu, mataimakin shugaban daga cikinta.

Amma a watan Maris, Mr Adams Oshiomhole, ya sanar da yafe musu laifukan da ya ce sun yi na zagon-kasa ga jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *