December 11, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutum 150 Suka Mutu Yayin Wata Zanga-zanga

2 min read

Adadin wadanda suka mutu a yankin Oromia na kasar Habasha yayin da ake boren da ya samo asali daga kisan gillar da aka yi wa wani fitaccen mawaki ya kai mutum 150.

Kisan Hachalu Hundessa wanda ya yi fice a fannin wakokin siyasa, ya kara zafafa rikicin kabilanci a kasar Habasha, yayin da wannan zanga zanga ta isa yankin Oromia wato maihafar mawaki Hundessa.

Fisseha Tekle, mai bincike ne a kungiyar kare hakin bil’adama ta Amnesty International ya ce, “Binciken farko da muka gudanar, ya nuna cewa jami’an tsaro na harbin masu zanga zanga saboda suna kona taya ko kuma suna rusa gine-ginen gwamnati, mun lura cewa jami’an ba sa bin ka’idojin da aka shimfida masu na gudanar da aikinsu.”

Mafi aksarin mace-macen an same su ne a yankin Oromia yayin da wasu kuma sun faru ne a Addis Ababa, babban birnin kasar ta Habasha.

‘Yan sanda sun ce sun kama akalla mutum 2,000. Hukumomin kasar sun katse hanyoyin intanet da na wayoyin salula a wani yunkuri na kashe wutar rikicin, wani abu da ya sa masu bibiyar hakkokin jama’a ke shan wuya wajen gano asalin adadin wadanda suka mutun.

A dai ranar Litinin 29 ga watan Yuni aka harbe mawaki Hundessa da daddare a birnin na Addis Ababa.

Kisan na zuwa ne mako guda bayan da Hundessa ya bayyana a wani shiri, inda ya yi ta caccakar shugabancin kasar tare da yin Allah wadai da garkame matasan Oromo da hukumomi suke yi.

Shi dai mawakin dan Oromo ne, kabilar da tarihi ya nuna cewa an dade ana nuna mata wariya a kasar ta Habasha.

‘Yan sandan kasar sun ce suna tsare da mutum uku da ake zargi suna da hannu a kisan mawakin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *