Yan bindiga 200 sun kashe mutum 15 a Katsina
1 min read
Rahotanni daga kauyen ‘yar Gamji da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga kusan 200 dauke da makamai sun kai hari inda suka kashe mutane fiye da 15.
‘Yan bindigar wanda suka je a babura sun kashe manoman da suka tarar a gona ne.