July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Za mu ɗauki mataki kan harin jirgin Majalisar Ɗinkin Duniya

2 min read

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da harin da ‘yan Boko Haram suka kai wa jirgi mai saukar ungulu na Majalisar Ɗinkin Duniya.

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasar ya fitar kan harkokin watsa labarai Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce “za mu ɗauki mataki kan harin da aka kai da ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyu har da jinjiri ɗan shekara biyar”.

Sanarwar ta shugaban ƙasar na zuwa ne bayan Majalisar Ɗinkin Duniyar ta yi kira ga gwamnatin ƙasar ta gudanar bincike kan harin tare da gaggauta hukunta waɗanda suka aikata laifin.

Shugaban ya kuma yi kira ga ma’aikatan bayar da agaji da ke aiki a yankin arewa maso gabas ta a kowane lokaci sun rinƙa shirya tafiye-tafiyen su – ta jirgi ko mota tare da haɗin kan jami’an tsaro.

Tun a ranar Asabar ne dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah wadai da wannan hari da ƙungiyar Boko Haram ta kai kan ɗaya daga cikin jiragenta masu saukar ungulu a yankin Damasak na jihar Borno a arewa maso ƙasar.

Lamarin ya faru ne ranar 2 ga watan Yuli kuma ko da yake babu abin da ya faru da ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniyar, amma ya yi sanadin mutuwar mutum biyu, ciki har da yaro ɗan shekara biyar, a garin na Damasak.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Asabar, shugaban sashin jinƙai na hukumar da ke Najeriya Edward Kallon ya bayyana cewa harsasai da ‘yan tayar da ƙayar bayan suka harba wa jirgin ya lalata shi kuma ya tsayar da ayyukan jinƙai da ake yi a yankin na arewa maso gabas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *