An fitar da jadawalin jarrabawar WAEC
1 min read
Hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma, WAECE,ta fitar da jadawalin shekarar 2020. Babban jami’in hukumar Mr. Patrick Areghan ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, babban birnin kasar. “An aika jadawalin karshe na WAEC ga ofisoshin yankuna da rassa ga makarantun ilimi da ma’aikatu na gwamnatin tarayya da jihohi,” in ji babban jami’in. Ya jaddada cewa za a gudanar da jarrabawar ne ranar 3 ga watan Agusta sannan a kammala 5 ga watan Satumba. Ya ce dalibai 1,549,463 ne za su rubuta jarrabawar daga makarantu 19, 129 da ke fadin kasar, yana mai gargadi ga dalibai su guji satar jarrabawa.