June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

DSS Ta Musanta Kama Shugaban EFCC

1 min read

Jami’an tsaron DSS a Najeriya sun musanta kama shugaban EFCC, Ibrahim Magu kamar yadda rahotanni na baya-bayan nan suka bayyana.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun kakakinta Peter Afunanya.
“Muna so mu sanar da jama’a cewa DSS ba ta kama shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Ibrahim Magu ba, kamar yadda kafofin watsa labarai suka bayyana.”
Wasu rahotanni na daban sun bayyana cewa an tafi da Magu domin fuskantar wani kwamiti wanda shugaban kasa ya kafa domin duba wasu zarge-zargen da ake yi masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *