June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Fadar shugaban Najeriya ta dakatar da shugaban EFCC

1 min read

Wata majiya mai karfi da ta bukaci a sakaya ta daga Fadar shugaban Najeriya ce ta tabbatar wa da BBC Hausa hakan a ranar Talata.

A ranar Litinin ne Ibrahim Magu ya bayyana a gaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na aikata ba daidai ba.

Cin hanci ne ya jawo Coronavirus – Magu
Bincike kan Magu: Abubuwan da muka sani kawo yanzu
Kwamitin – karkashin jagorancin tsohon mai shari’a Ayo Salami – ya gayyaci Mr Magu ne domin jin ta bakinsa kan abubuwan da suka shafi jagorancinsa a hukumar ta EFCC.

Wasu majiyoyi a Najeriya sun tabbatar cewa Magu ya kwana a tsare a hannun jami’an tsaro saboda ba a kammala binciken da aka soma ba a ranar Litinin.

A ranar ta Litinin ne rahotanni suka nuna cewa jami’an tsaron DSS a kasar sun kama Ibrahim Magu.

Sai dai wata sanarwa da DSS da kuma EFCC suka fitar daban-daban sun ce ba kama Mr Magu ta yi ba.

EFCC ta ce ya amsa gayyatar jami’an tsaro ne kawai, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *