July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Najeriya ta yafe wa gidajen rediyo kashi 60 na bashin da ake binsu

2 min read

Gwamnatin Najeriya ta sanar da yi wa gidajen rediyo da talbijin rangwamin kashi 60 cikin 100 na basukan da ta ke binsu.

Gwamnatin dai tana bin wasu kafafen watsa labarai na rediyo da talabijin bashin kudade da ya kai naira biliyan bakwai da miliyan dari takwas.

Cikin wata sanarwa, ministan yada labaran kasar Lai Muhammad ya ce gwamnati ta dauki matakin ne don rage musu radadin rashin kudaden shiga saboda annobar cutar korona.

A cewar Lai Muhammad duk wadanda ake bi bashin su hanzarta biyan kashi arba’in cikin dari na abin da ake binsu cikin watanni uku.

Sanarwar ta kara da cewa gidajen rediyo da dama a Najeriya ana binsu bashi mai yawa lamarin da yasa wasu ma ke fuskantar barazanar kin sabunta musu lasisin su.

Hajiya Sa’a Ibrahim, Shugabar Kungiyar kafafen watsa labarai na rediyo da talbijin a Najeriya kuma shugabar gidan talbijin na Abubakar Rimi a Kano ta ce sun yi farin ciki da wannan matakin.

“Ko ya ya idan aka yi maka abu, dole za ka yaba za ka ji dadi, abin da yake akwai shi ne an yi abin da za a ce ai da babu gwara ba dadi,”

“Wannan ma tun da ya wuce rabi za a ce an yi hobbasa toh amma dai abin da yake akwai shi ne dole za a bibiya kowa ya ma san matsayin bashin da yake kansa, kafin mu tafi biya din,” in ji Hajiya Sa’a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *