April 15, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Labarin Wasanni

2 min read

Kocin Chelsea Frank Lampard na son dauko dan wasan tsakiya na West Hamda Ingila Declan Rice, mai shekara 21. (Times – subscription required)

Manchester City da Manchester United suna son dan wasan baya na Napolida Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, da kuma dan Milan Skriniar, da ke taka leda a Inter Milan da Sloviakia. (Independent)

Chelsea da Real Madrid na son shan gaban Manchester United da Paris St-Germain kan dan wasan tsakiya na LazioSergej Milinkovic-Savic mai shekara 25. (Gazzetta dello Sport, via Express)

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya shaida wa dan wasan baya na Bournemouth Nathan Ake cewa yana son bahago a tattaunawar da suka yi bayan an tashi wasan da suka fafata a inda Manchester ta yi nasara da ci 5-2 a Old Trafford ranar Asabar. (Telegraph)

Crystal Palace na tunanin ware fam miliyan £25m kan dan wasan gaba na Celticda Faransa Odsonne Edouard, mai shekara 22. (Sun)

Man City na iya sayen Lionel Messi
Tottenham ta ci Everton 1-0 inda Lloris da Son suka kusa dambatawa
Bayern Munichza ta bar dan wasan baya na Austria David Alaba, mai shekara 28 ya yanke shawara kan makomarsa idan kwangilar shi ta kawo karshe 2021, idan zai ci gaba da kasance da kulub din ko kuma zai koma Premier League. (Mirror)

RB Leipzig na jiran dan wasan Faransa mai shekara 21 Dayot Upamecano, da ake alakantawa da Arsenal, ya tsawaita kwangilarsa idan ta kawo karshe a 2021. (Mirror)

Juventus na diba yiyuwar karbo dan wasan Chelsea da Italiya Jorginho, mai shekara 28. (Tuttosport, via Sun)

Real Madrid ba za ta saye sabbin ‘yan wasa ba saboda tasirin annobar korona, maimakon haka tana fatan ta samu kudi da ya kai fam miliyan £190 daga ‘yan wasan da take son rabuwa da su da suka hada da dan wasan gaba na Wales Gareth Bale, mai shekara 30. (Marca, via Star)

KocinReal Madrid Zinedine Zidane shi ne dalilin da ya sa dan wasan Morocco Achraf Hakimi, mai shekara 21, ya bar kulub din ya koma Inter Milan, a cewar wakilin dan wasan mai buga baya. (Marca)

Tsohon dan wasan Ingila John Terry, wanda shi ne mataimakin kocin Aston Villa Dean Smith, yana cikin wadanda ake tunanin Bristol Cityza ta ba aikin horar da ‘yan wasanta. (Football Insider)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *