Mazauna Unguwar Kurnar Asabe sun tashi wani iftila’i
1 min read
Al’ummar Unguwar Kurna Asabe dake cikin karamar Hukumar Dala a nan Kano,sun gudanar da wata l zanga-zanga a sakamakon ambaliyar ruwan sama a da ya fara addabar suyankin, a baya-bayannan.
Zanga-zangar wace ta gudana a jiya ta kunshi manya da yara dauke da kwalaye, da ke cewa wajibine gwamnati ta kawo mana dauki a yankin namu.
Wakilin Bustandaily ya zanta da daya daga cikin jagororin da suka shirya zanga-zangar wanda kuma ya nemi a boye sunan sa, ya ce wajine mufito mu nunawa gwamnati irin matsalar da muke fuskanta a yankin.
Shugaban ya kara da cewa da munar bana ta kankama wanda ya zuwa yanzu ruwa ya ci wasu daga cikin gidaje a yankin tare da baranar faduwar wasu daga cikin su.
Harwa yau shugaban ya ce cututtuka kan iya samun al’ummar yankin kasancewar ruwa na haduwa da shara wanda hakan abune mafi sauki wajen kamuwa da cututtuka.
Wasu Dattawa a yankin wanda suna daya daga cikin mutanen da ambaliyar ta fadawa sun bayyana kukun su,da gwamnatin Kano da sauran masu ruwa da tsaki domin kawo musu tallafi.
Daga fara damunar bana dai Jihar Kano,na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a wasu sassan Jihar wanda al’ummar ke kira ga gwamnatin da ta kawo musu daukin gaggawa.