Gwamnatin tarayya ta ce baza gudanar da jarabawar Waec.
1 min read
Gwamnatin Najeriya ta soke matakin bude makarantu ga daliban da zasu rubuta jarabawar WAEC a wannan shekarar.
WASHINGTON, D.C. —
Ministan harkokin ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da yayi da manema labarai da yammacin yau.
Adamu ya ce makarantu ba zasu bude ba har sai an tabbatar da cewa Covid-19 ba za ta iya yi wa dalibai illa ba.
Ya kara da cewa, babu makarantar da za ta yi WAEC a Najeriya a wannan shekarar.
Hakan na zuwa ne bayan da Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana a ranar Litinin cewa za a gudanar da WAEC a cikin watannin Augusta da Satumba.
gaskiya ba,ai mana adarciba ace dalibai shikenan a haka zasu dauwama a gidajin su ba makarantu ba,aikinyi musan manma mu na Jami,ai da muka fara karatun 2020 ayinzu da muna zuwa schools da tini mun gama nce 2 second semistar karshe na leave 2 gashi yanzu muna gida ba aiki dan Allah government ta duba mana tayi mana adarci
Allah yasa gwamnati taji