June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yadda Aka Bude Filayen Jiragen Sama a Najeriya

1 min read

Sai dai hakan ya biyo bayan shimfida wasu ka’idojin kariya daga kamuwa da cutar wanda cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasar NCDC ta fitar da kuma hukumar sufurin jirage ta kasar.

Daya daga cikin jiragen da suka sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa wato Nmandi Azikwe Int’l Airport dake babban birnin tarayyar kasar Abuja, daga Legas ya taso.Yanzu jihohi biyu ne gwamnatin kasar ta ba da umarnin filayen jiragensu su soma aiki daga ranar 8 ga watan Yuli, tun bayan sama da watanni uku da aka dakatar da duk wata zirga zirga da ta shafi jiragen.

A cewar Kyaftin Rabiu Yadudu da ke zama babban shugaban hukumar filin jirgin sama ta Najeriya, “an dauki matakai da dama kuma an bai wa ma’aikata da ke wajen horo na musamman kana a shirye suke don tabbatar da an kare lafiyar al’umma.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *