June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan fashin daji sun sake auka wa ƙauyukan Zamfara da Sokoto

1 min read

Ɗumbin mutane ne rahotanni suka ce sun tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren ‘yan fashin daji a yankunan Isan jihar Sokoto da ma na Zamfara mai maƙwabtaka tun daga farkon wannan mako.

Bayanai daga ƙaramar hukumar Shinkafi sun ce gomman mutane ne suka fantsama manyan garuruwan yankin kamar ita Shinkafin don kuɓuta da rayukansu.

Wata shaida da ta tsere daga ƙauyen Kamarawa ta faɗa wa BBC daga inda ta fake a cikin daji cewa sun baro gidajensu ne lokacin da suka ga mahara na far wa mazajensu tare da yin awon gaba da dabbobi.

“A jiya (Litinin) da safe, sai muka ga jiragen sama suna ta yawo a yankinmu, sai suka sauka jejin da ɓarayin suke, suna ta sako musu bom-bom da bindigogi. Ga sojoji daga sama suna ta yin shuuu,” in ji matar.

Ta ce sun yi ta murna don kuwa suna tunanin wahala ta yanke musu. “Muna cewa ƙila za a ɗauke mana mutanen nan ne.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *