July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Babu uziri cikin bayyana tsiraici ga mata – Sheikh Pantami

2 min read

Wani fitaccen malamin addinin Musulunci kuma minista a Najeriya, ya ce babban abin tsoro ne, ƙaruwar saɓon Allah kamar aikata fyaɗe a daidai lokacin da duniya take fama da annoba.

Dr. Isa Ali Pantami ya ce matsalar ƙaruwar fyaɗe baya-bayan nan a sassan ƙasar, “annoba ce ta shigo cikinmu kuma jarrabawa ce, bala’i ne kuma”.

“Abin da ke ba ni tsoro, lokacin da ya dace mu ƙara ƙasƙantar da kanmu, mu koma zuwa ga Allah (SWT)” in ji malamin amma ayyukan laifi suna ƙara yawa. “Bil haƙiƙa, wannan bala’i ne”.Sheikh Pantami ya bayyana haka yayin wata zantawa da wakilin BBC Haruna Shehu Tangaza.

Ya ce ba hujja ba ce mutum ya auka wa mace don kawai ta sanya tufafin da yake jin suna fito da tsiraici. “Addini ya wajabta maka, ka runtse ganinka,” in ji Panatami.

A cewarsa, idan wata ta fito waje ko da tsirara take yawo, tsanani mutum ya kawar da kai, ya nemi tsarin Allah. Kada ya ƙara kallo.

Duk da haka, malamin ya ce su ma mata akwai haƙƙi kansu na yin shigar kamala. Da kuma guje wa aikata duk abin da zai ja hankalin wani matuƙar yin hakan bai kamata ba.

A baya-bayan nan dai, al’ummar Najeriya na ci gaba da bayyana damuwa saboda ƙaruwar ayyukan fyaɗen da ake samu a kan mata da ƙananan yara, lamarin da ya kai ga kiraye-kirayen a ƙara tsananta hukunci.

Lamarin da shi ma malamin ya nanata, inda yana da kyau a ƙarfafa dokoki a kan batun fyaɗe sannan a tabbatar ana aiki da su kan mutanen da kotu ta kama da laifi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *