September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Labarin Wasanni saura maki daya tsakanin Madrid da Barcelona

2 min read

Barcelona ta rage tazarar da ke tsakaninta da Real Madrid, bayan da ta doke Espanyol da ci 1-0 a gasar La Liga ranar Laraba.

Barcelona wadda ta karbi bakuncin Espanyol a wasan mako na 35 a Nou Cmp ta ci kwallon tilo ta hannun Luis Suarez kuma na 15 da ya zura a raga a bana.

Fati zai kafa tarihin cin kwallo a matsayin matashi a Spaniya
Man City ta ragargaji Newcastle United a Premier

Sai dai kuma kungiyoyin sun kammala karawar da ‘yan kwallo 10 kowacce a fili, bayan da aka bai wa Ansu Fati jan kati da dan wasan Espanyol Pol Lozano.

An kori matashin dan wasan Barca, Ansu Fati kan keta da ya yi wa Fernando Calero, minti uku tsakanin aka sallami Pol Lozano na Espanyol kan yin keta da mugun nufi. .

Da wannan sakamakon Barcelona ta hada maki 76 a wasa 35 da ta buga a La Liga, bayan da Real mai maki 77 ta yi karawa 34.

Sai a ranar Juma’a ne Real Madrid za ta karbi bakuncin Deportivo Alaves a wasan mako na 35.

Barcelona da Espanyol wacce take ta karshen teburi sun buga 2-2 a wasan farko a cikin watan Janairun 2020 a gasar shekarar nan.

Kungiyar ta Nou Camp ta ci karo da koma baya ne, bayan da ta yi canjaras uku a La Liga ta bana da aka ci gaba da gumurzu tun bayan watan Maris.

Barcelona ta je ta buga 0-0 da Sevilla, sannan ta yi 2-2 a gidan Celta Vigo ta kara 2-2 a gidanta da Atletico Madrid.

Saura wasa uku Barca ta karkare gasar La Liga wacce ita ke rike da kofin bara, za kuma ta je gidan Valladolid ranar Asabar a karawar mako na 36.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *